J N I SAMINAKA Coronavirus ta janyo cacar baki tsakanin Ganduje da El-Rufai

Ad Code

Coronavirus ta janyo cacar baki tsakanin Ganduje da El-Rufai

El-rufai da Ganduje alama sakonnin da gwamnan jihar Kaduna da ke Najeriya, Malam Nasir El-Rufai, ya rika wallafa a shafinsa na Twitter a baya-bayan nan inda ya ce almajirai da dama da suka kamu da cutar korona a jiharsa wadanda Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano ya koma da su Kaduna ne sun bata wa Ganduje rai.
A makon jiya Gwamna El-Rufai ya wallafa wani sakon Twitter inda ya ce galibin masu dauke da cutar korona a jihar almajirai sama da gwamnatin Kano ta koma da su Kaduna.
Hasalima a sakon da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar 4 ga watan Mayu, ya ce a cikin mutum 72 da suka kamu da cutar a ranar, "kashi 65 almajirai ne da aka dawo da su daga jihar Kano."
Sai dai gwamnatin Kano ta ce ba da gangan take mayar da allmajiran jihohinsu ba.
Wata sanarwa da Malam Abba Anwar, mai magana da yawun Gwamna Ganduje ya aike wa manema labarai ranar Lahadi, ya ce dukkan gwamnonin jihohin arewacin Najeriya sun amince su mayar da almajirai jihohinsu na asali kafin su dauki matakin.
"Mun amince a wurin taron Kungiyar Gwamnonin Arewa cewa ya mayar da almajirai jihohinsu na asali. Shi ya sa muke kai su jihohinsu da kyakkyawar niyya da kuma tari, dukkan almajiran da ba 'yan Kano ba ne mu kai mus jihohinsu na asali," a cewar Malam Anwar.
Ya kara da cewa bai kamata a rika mayar da batun siyasa ba.
Gwamna Ganduje ya kara da cewa: "Yadda muke mayar da almajirai jihohinsu, haka mu ma ake dawo mana almajirai 'yan asalin jihar Kanodaga wasu jihohin. Don mu ba ma yin surutu a kan batun ba ya nufin dukkansu lafiyarsu kalau ba sa dauke da COVID-19."
Gwamnan na Kano ya tabbatar da cewa wasu daga cikin almajiran da aka koma da su Kano suna dauke cutar korona, yana mai cewa "amma mu ba mu mayar da batun siyasa ba. Saboda mun yi amannar cewa ba surutu muke bukata ko neman suna yanzu ba. Abin da suke bukata a wannan mawuyacin hali shi ne kulawa."
Da ma dai masana harkokin lafiya a Najeriya sun ja kunnen mahukunta da su daina amfani da siyasa a yakin da suke yi da cutar korona, domin kuwa hakan zai sa mutane su ci gaba da mutuwa yayin da 'yan siyasa suke ce-ce-ku-ce da juna kan matakan da suka dace don dakile cutar.

Post a Comment

0 Comments

J N I SAMINAKA