J N I SAMINAKA HANKALI SA YA TASHI

Ad Code

HANKALI SA YA TASHI


Wata rana an sacewa shehu kudi kimanin jaka biyu , said ya tafi masallaci ya dukufa tun farkon dare har gari ya waye, yana rokon Allah ya dawo masa  da kudinsa. Sai aka dace a wannan lokacin wani daga cikin attajiran garinsu ya kasance yana halin tafiya a jirgin ruwa. Sai iska mai karfi ta taso tana Neman ta kifar da jirgin , sai attajirin nan yayi bakance cewa idan ya kubuta daga halaka , yadawo gida lafiya , zai bawa shehu jaka biyar saboda Allah. Allah da ikonsa sai kuwa ya hana afkuwar wannan hadari, attajiri ya tsira yana isowa gida sai ya nemi shehu ya danka masa kudin da yayi bakance. Ya labarta masa abinda ya faru, yace ai Allah ya tseratar danine Albarkacin adduar Ku Allah ya saka da Alheri.
  Da mutumin ya tafi sai shehu yayi shiru yana tunani game da wannan abu sannan yace : Allah da iko yake ! Yanzu da wani mutum na bawa rancen wanan kudi da ya dawo min dashi batareda nashiga wani tashin hankali ba?
   Kai !hankalin Dan Adam dai baya gane sirrin fake cikin hikimar Allah mai girma da buwaya , dubi dai yadda kudi na suka bata da yadda suka dawo!!!
.
.
Shehu jaha

Post a Comment

0 Comments

J N I SAMINAKA