BISMILLAHI ARRAHMAN ARRAHIM
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki mai kowa mai komai, mai bawa kowa komai ba shi da bukatar komai a gurin kowa, kowa ke da bukatar komai a gurinSa. Tsira da Amincin da Salati da Taslimi su kara tabbata ga Shugabanmu Annabi Muhammadu (S.A.W), da Iyalan Gidansa tsarkaka, da Sahabbansa wadanda suka bi shi da kyau da kyautatawa da duk wanda ya bi tafarkinsa har izuwa ranar sakamako. Bayan haka, kamar yadda mu ka yi alkawarin ci gaba da kawo muku tarihin iyayyen muminai tun daga kan uwar muminai Nana Khadija (Allah ya kara mata yarda) har zuwa kan uwar muminai Nana Maimunah (Allah ya kara mata yarda), cikin nufin Ubangiji ga shi yau za mu fara. In sha Allahu kuma za mu rika gabatar muku da wannan tarihin a duk ranar Litinin cikin wannan jarida mai albarka ta Leadership Ayau. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya da fa mana, ya bamu daman ganin gaskiya da kuma riko da ita, kana kuma ya bamu daman ganin karya da kuma watsi da ita, koda kuwa daga wajen wane ne ta fito. Shinfida Ya mai karatu, rayuwar Annabi (Sallalahu Alaihi Wassalam) ta kasance abar koyi ce ga muminai, kamar yadda Allah ya ce: “Hakika abin koyi kyakkyawa ya kasance a cikin (rayuwar) Manzon Allah ga wanda ya kasance yana kwadayin Allah da ranar lahira, kuma ya ambaci Allah da yawa.” Suratul Ahzab. Ayyukan sa (Sallalahu Alaihi Wassalam) sun kasance mabubbuga ne cikin mabubbugan shari’ar musulunci mai mahimmanci, domin haka ne ya zama wajibi a samu wanda zai rawaito mana hukunce-hukuncen shari’a a gidan Annabta mai tsarki na yadda ake rayuwa da iyali da mata, da hukunce-hukuncen da ya kebanci muminai mata ne kawai a zamanin su, dama bayan zamanin su har zuwa ranar alkiyama. Kamar yadda Annabi (Sallalahu Alaihi Wassalam) ya karantar da su, to suma sun cancanci su kasance ababan koyi ga mata muminai a kowanne zamani, wannan shi ne abin da ya faru, godiya da baiwa ta Allah ce, sun kasance ababan koyi ga dukkan muminai mata, wannan shi ma ya kasance cikin hikimar yawaita auren sa (Sallalahu Alaihi Wassalam). Kamar uwar muminai Nana Aisha (Allah ya kara mata yarda), daya daga cikin iyayyen muminai, babba ce cikin wadanda suka rawaito hadisi daga Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wassalam). Haka nan yana daga hikimar yawan auren Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wassalam) hada alaka mai karfi da kabilun Larabawa a farkon musulunci, saboda da’awar musulunci ta fadada, kamar misalin aurensa ga Nana Juwairiyyah (Allah ya kara mata yarda), sai sababin wannan aure ya sanya musuluntar Kabilar Banu Musdalik. Haka nan yana daga cikin hikimar yawan aurensa (Sallalahu Alaihi Wassalam) domin ya kara karfin alakarsa ga Sahabbansa, kamar Sayyadina Abubakar da Umar (Allah ya kara yarda a gare su) hakika ya auri ‘ya’yan su, Nana Aisha da Nana Hafsah (Allah ya kara musu yarda), kamar yadda ya girmama Sayyadina Usman da Sayyadina Ali da daura musu aure da ‘ya’yansa. Haka nan auren wasun su da ya yi ya kasance domin tabbatar da hukuncin shari’a da ba ta hukuncin Jahiliyya, kamar hukuncin mutum ya haramtawa kan sa auren matar da yaronsa ya aura wanda ba dan sa na cikin sa ba ya saka, shi yasa ya auri Zainab ‘yar Jahsh (Allah ya kara mata yarda). Haka nan yana daga hikimar yawan aurensa, ya auri wasu daga matansa domin duba ga wani halin da suke ciki na zamantakewa, kamar uwar muminai Saudah ‘yar Zam’ah (Allah ya kara yarda a gare ta) mijin ta ya rasu, haka nan Ummu Salamah (Allah ya kara yarda a gare ta) mijinta ita ma ya rasu ya bar ‘ya’ya marayu, haka nan Ummu Habiba (Allah ya kara yarda a gare ta) da mijin ta ya yi ridda a kasar Habasha, sai ta zauna zaman bakunta, domin haka dukkan wannan auren Annabi (Sallalahu Alaihi Wassalam) ya yi shi ne saboda taimaka musu. Masu gur batacciyar fahimta kafirai da munafikai suna cewa: “Wai Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wassalam) ya yi wannan aure ne domin ya kosar da bukatarsa ta sha’awa ga wadannan matan! Ta yaya za a yarda da wannan mummunar maganar alhalin uwar muminai Nana Aisha ce kawai cikin su budurwa, ragowar gaba dayan su duk zawarawa ne masu ‘ya’ya da yawa, wannan yana nisantar da tunanin cewa ya auri wadannan matan ne saboda kosar da sha’awar sa, domin da haka ne, to da sai ya yi ta auran budurwai. Wace ce uwar muminai Khadija? Ita ce Khadija ‘yar Khuwailid Dan Asad Dan Abdul Uzza Dan Kusay, ta na daga cikin manyan matan Kuraishawa kana kuma wacce ta fi su kyau, tun kafin Musulunci ma ana kiranta da suna At-Tahira (tsarkakakkiya) saboda irin kyawawan danbi’unta, kuma ana kiranta da Shugabar matan Kuraishawa. Irin wannan kyawawan halaye na ta da kuma irin daukakan da take da shi ya sa wasu daga cikin manyan Kuraishawa, irin su Sha’ibata Dan Abu Rabi’a, Utubatu Dan Abu Mu’ai’din, Abu Jahil Dan Isham, Faisatu Dan Abu Yahabin, da dai sauransu, suka bukaci aurenta da kuma nuna mata kudi, amma taki amincewa, a karshe ta zabi Shugabanmu Annabi Muhammadu (Sallalahu Alaihi Wasalam) saboda halayensa na kwarai da ta gani. Auren ta na Farko Uwar muminai Nana Khadija kafin ta auri Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wassalam) ta auri Abu Halah Dan Zurarah Attaimiy, ta haifa masa ‘ya’ya biyu, Hindu da Halah, bayan sa ta auri Atik Dan Abid Almakhzumiy, ta haifa masa ‘ya daya mace mai suna Hindu. Imamu Zahabiy ya ce: “Khadija ta fara auren Abu Halah Dan Zurarah Attaimiy, sai bayan sa ta auri Atik Dan Abid Dan Abdullahi Dan Umar Almakhzumiy, sannan bayan sa ta auri Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wassalam), ya tare da ita yana dan shekara ishirin da biyar, ta kasance ta girme shi da kusan shekaru goma sha biyar.” Fat’hul bariy (7/134). Assiyar (2/111). To kamar yadda muka fadi, uwar muminai Nana Khadijah mace ce mai dukiya, kana kuma tana son wanda zai kula mata da wannan dukiya ta ta cikin aminci ba tare da cuta ba, don haka sai ta bukaci Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasalam) wanda daman tun zamanin Jahiliyya mutanen Makka suna kiransa ‘As- Sadikul Amin’ da ya kula mata da wannan dukiya nata. Bayan wannan yarda da Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasalam) ya yi da wannan bukata ta uwar muminai Nana Khadijan, sai suka fita kasuwanci tare da wani bawanta mai suna Maisara. A yayin wannan fatauci dai an sami riba mai yawan gaske, hakan kuwa saboda albarkar da ke tare da Ma’aikin ne da kuma gaskiyarsa. To bayan dawowarsu, da kuma irin labarin da wannan bawan nata ya bata dangane da irin kyawawan halaye na Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasalam), nan take sai so da kaunarsa ta cika zuciyar uwar muminai Nana Khadijah, inda ta bukaci ya aure ta.Read


0 Comments