Kun kwana da sanin hukuncin kisa da wata Kotun Shari'ar Musulunci ta yanke wa wani mawaƙi a Jihar Kano saboda ɓatanci ga Annabi SAW.
A Najeriyar dai mafi yawan mutane hukuncin ya yi musu dadi yayin da wasu kuwa ba su ji daɗin hukuncin ba, kamar yadda suka yi ta bayyana wa a shafukan sada zumunta.
Wannan ba abin mamaki ba ne idan aka duba cewa Najeriya cike take da mabiya addinai da ƙabilu daban-daban, hakan ya bayyana ƙarara a dandalin Twitter.
Wanda ya jagoranci zanga-zangar neman a hukunta mawaƙin mai suna Yahaya Aminu Sharif, Idris Ibrahim ya shaida wa BBC cewa "mun ji daɗin hukuncin kuma izina ce ga sauran jama'a wadanda ke son bin hanya irinta Yahaya"
Yadda tattaunawar take gudana
Da dama daga cikin ra'ayoyin da jama'a suka bayyana na cin zarafi ne ga addinai da kuma wasu abubuwa masu tsarki, waɗanda BBC ba za ta iya wallafawa ba.
Maudu'ai irin su #Islam da #Kano da #Shari'a da #Mohammed (Annabi Muhammad S.A.W.) da #BokoHaram da #Blasphemy (saɓo) da #Christians (Kiristoci) da #Quran da #Religion (addini) duka suna cikin abubuwa da ake tattaunawa a kansu a Twitter.
An yi amfani da maudu'in #Islam sau fiye da 120,000 - mafi yawa a cikinsu - sai #Blasphemy fiye da 31,000, #Kano fiye da 35,000, Muhammad fiye da 41,000, #Qur'an fiye da 32,000, #Sharia fiye da 16,000.
Kazalika kalmar 'Blasphemy' ce ta biyar a matsayin wadda 'yan Najeriya suka fi neman ƙarin bayani a kanta a shafin Google Trend na matambayi-ba-ya-ɓata, inda aka nemi ƙarin bayani a kanta sau fiye da 5,000.
Kalmar blasphemy tana nufin furta kalaman ɓatanci ga wani abu na addini da ake girmamawa ko kuma saɓo a taƙaice, wadda da ita kafafen yaɗa labarai na Ingilishi suka riƙa bayar da rahoton hukuncin kisan.

0 Comments