J N I SAMINAKA KONA ALKUR'ANI YA JANYO TASHIN HANKALI A SWEDEEN

Ad Code

KONA ALKUR'ANI YA JANYO TASHIN HANKALI A SWEDEEN

Wasu masu fafutika sun ƙona Al-Kur'ani mai tsarki a garin Malmo na ƙasar Sweden, abin da ya jawo zanga-zanga tare da tashin hankali ranar Asabar. Kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito masu zanga-zangar kusan 300 sun cinna wuta a kan tituna tare da jefa abubuwa a kan 'yan sanda a daren Juma'a. An jikkata 'yan sanda 15 sannan an kama mutum kusan 15. An ƙona Kur'anin ne da tsakar ranar Juma'a a kusa da wata unguwa ta 'yan cirani da wasu masu tsaurin ra'ayi suka yi sannan suka wallafa bidiyon a intanet, a cewar kamfanin dillancin labarai na TT. AP ya ce an kama mutum uku bisa zargin haddasa ƙiyayya ga wani rukunin al'umma ta hanyar ƙona Kur'ani - littafin da al'ummar Musulmi ke girmamawa a matsayin mai tsark

Post a Comment

0 Comments

J N I SAMINAKA