Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tuhumi sojojin rundunar hadin gwiwa a filin Maimalari Cantonment da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno, da su kara kaimi wajen yaki da matsalar rashin tsaro da ke addabar yankin Arewa maso Gabas da sauran sassan kasar.
Buhari ya bayar da wannan umarnin ne a ranar Alhamis yayin ziyarar da ya kai jihar.
Da misalin karfe 10 na safiyar Alhamis.
Buhari ya tabbatarwa da sojojin kasar karin samar da kayan yaki.
"Bai kamata mu bar abokan gabanmu ko masu aikata laifi su lalata mana ikon mallaka ba."
"Yayin da nake yaba muku, bari na fada muku cewa har yanzu akwai sauran aiki a gaba a yankin Arewa maso Gabas, Yamma da kuma kasar baki daya."
Daga baya shugaban ya ziyarci wurin da ake kula da sojojin da suka ji rauni don tausaya musu.
Ana kuma sa ran Buhari zai kaddamar da wasu ayyukan da gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum ya aiwatar


0 Comments