An kashe daya daga cikin daliban da ‘yan fashi suka sace a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin-Yauri a jihar Kebbi.
Abubakar AbdulKadir, mataimakin kwamandan rundunar hadin gwiwa a shiyyar arewa maso yamma, ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Juma’a.
Ya kuma kara da cewa wasu mutum biyar da suka hada da dalibai hudu da wani malami sun samu kubuta daga hannun 'yan fashin.
Har yanzu ba a tabbatar da yawan daliban da ‘yan bindigar suka sace yayin harin a ranar Alhamis da rana ba.


0 Comments